.
📻 Labaran Hausa

Asalin kayan gwanjo da inda ake samun su… Chef Bashir BNG

Asalin kayan gwanjo da inda ake samun su... Chef Bashir BNG

Asalin kayan gwanjo da inda ake samun su… Chef Bashir BNG

Da farko zan fara da magana akan post dina na farko wanda wasu su ka dauka kayan gwanjo a bola ko shara ake samo su, sam ba haka bane, ba inda na fadi hakan, kawai dai na ce ganin wadannan kayan a bola ya tuno min da wani post da na dade ia son yi akan asalin kayan gwanjo da inda ake samunsu, kawai abin da na fada kenan, amma abun mamaki duk da na ce za yi bayani a wani post din, amma tuni wasu har sun yanke hukuncin cewa daga bola kayan gwanjo suke ake kawo su Africa. Ina sake jaddadawa ban fadi hakan ba, kuma haka nake nufi ba. Zan bayani dalla-dalla, don haka wata kila post din zai dan yi tsawo, amma a daure a karanta har karshe, hakan zai sa ku san daga inda kayan gwanjon da ku ke siya suke zuwa muku har ku darar a gaba.

Ana samun kayan gwanjo daga sassa daban daban na duniya, amma ni zan yi bayani ne kawai a inda na fi wayo wato kasar Amurka. Babbar hanyar da kamfanonin gwanjo suke samun kaya ita ce, ta hanyar DONATION. Mafi yawanci kungiyoyin CHARITY, su suke tattaro kayan donation, sai su sayar wa da kamfanonin gwanjo, su dama wadannan charities din ba kayan suke so ba, kudi suke bukata, idan su ka sami kayan donation daga mutane ko stores din kaya, sai tura wa wadannan kamfanonin. Wasu charities din, su na ajiye irin wadannan manyan abubuwan da ku ke gani a hoton da ke kasa, duk wanda yake da kayan da zai bayar sai ya je ya zuba a ciki, ba shara ko bola bace, kaya ne masu kyau, wani lokacin idan aka sami jinkiri ba su zo sun kwashe kayan ba, shi ne za ku gansu har a kasa an ajiye musu. Saboda haka ba a bola suke ba, nan suna da tsari komai da muhallinsa, in har ka ga kaya a bola to baza a taba kai su kamfanin gwanjo ba, akwai yadda ake yi da irin wadannan kayan, san yi bayani a gaba. Wasu kuma charities din ana kiransu ne su je har gidan mutane da babbar motarsu su lodi kayan.

Kada ku dauka dan mutum ya ba da kayan da ya taba yin amfani da su ku dauka ba masu kyau bane, kaya ne ma su kyau, ni ma akwai matar da ta ke bani kayan jikanta, za ku sha mamaki, Wallahi wasu kayan baza ka ce an taba sa su ba, wasu kayan ma sabbi ne ko bude su ba a yi ba.

Wasu kayan gwanjon kuma sababbi ne, abin da ke faruwa shi ne, katinan sayar da kayan sawa, idan kaya su ka dade basu sayu ba, ga matakan da suke dauka akan kayan: na farko za su rage musu kudi wanda ake kira da “sale” bayan an gama, abin da yai saura ana yin wani abu clearance, shi wannan clearance din ana sake zabgewa kayan kudi ne, amma in ka siya baza ka dawo da su ka ce ka fasa ba, wasu stores din kuma bayan “sale” din su na kai kayan wasu stores da suke siyar da kaya da sauki irinsu TJ Maxx da Marshall’s dss. Idan a can ma kayan basu kare ba, to daga kuma sai su bayar da kayan ga charity, su kuma charity sai su sayarwa da kamfanonin gwanjo. Irin wadannan kayan sune kayan da ba a taba sa su ba, kuma sabbi ne.

Meye charity, su ne wadanda suke neman taimako domin tallafawa mabukata, kamar dai Foundation din da muke da su anan Facebook, duk wadannan a Amurka ba Foundation bane, ana ce musu Charity Organization, akwai bambanci tsakanin Foundation da Charity da kuma nonprofit organization. A shirye nake na karbi gyara in akwai.

Yanzu kun dai ji bayanin yadda ake samun kayan gwanjo a takaice, na takaita ne sosai, amma zan iya yin karin bayani a cikin comments in aka bukaci hakan, saboda haka ku bibiyi reply dina a cikin comments dinku. Yanzu kuma me ke faruwa a kamfanonin kayan gwanjo? Kamar yadda ku ke gani a hotunan da ke kasa, ba wai kawai karantawa na yi ba, ni ma ina taba harkar gwanjon tare da wasu manyan ‘yan gwanjo a kasuwar gwanjo ta Kano, hotuna da ku ke gani an dauke shi ne a shekarar 2012 a wani babban kamfanin gwanjo da ke jahar New Jersey sunan kamfanin Tranclo. Kafanonin gwanjo a Amurka suna da ma’aikata masu yawan gaske, wadanda suke tantance musu duk kayan gwanjo su ware grade A da grade B da C dss, sannan kuma su ware kayan da baza a iya sa su a kowanne grade ba, sun zama shara sai zubarwa, a sama ce zan gaya muku yadda ake yi da kayan da basu da kyau, in ku ka duba a hoto na hudu, akwai taswirar charts wannan zanen kadai ba ya bukatar dogon bayani daga hoton ko zanen za ku fahimci yadda ake tantance kaya wadanda su ka cancanci sake amfani da su wato su ke turowa oversea wato sun zama kayan gwanjo, akwai kuma wadanda ake konawa, kaso mafi tsoka sune wadanda ake bunnewa a inda aka rubuta “landfill”, in ku ka lura 4.3% ne kadai ake turawa kasashen duniya a matsayin kayan gwanjo. Matsalar kayan da ake bunnewa an ce zai dauki shekaru sama da 200 kafin su narke su zama kasa, hakan kuma illa ne ga kasar.

Afwan, na tsawaita, zan tsaya haka, amma akwai karin bayani dayawa da ban yi ba, misali yadda ake yi da kaya ma su tsada. Dan abin da zan kara shi ne, ina so mu sani cewa kayan gwanjo kusan babu inda ba a siyar da su a duniya, har anan Amurka, akwai kantina ko stores dayawa da suke siyar da kayan gwanjo ko second hand clothes, sai su kawai ba a shigo musu da kayan. Sannan kusan duk wata nahiya ta duniya ana shigar musu da kayan gwanjo: middle east, Europe, Asia, balle kuma Africa, sai dai har yanzu haramcin shigo da kayan gwanjo Najeriya ya na nan, ni dai ban san dalili ba, domin kayan basu wadace mu ba, amma me yasa aka haramta shigo da kayan?

Bashir Ibrahim Na’iya ©️

C.E.O_Founder_OF_Educatetimes _Auwal_Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button