Advertisement
📻 Labaran Hausa

Gwamnatin Najeriya ta sako wasu tsoffin gwamnoni da aka samu da laifin rashawa.

Gwamnatin Najeriya ta sako wasu tsoffin gwamnoni da aka samu da laifin rashawa.

Advertisement

Gwamnatin Najeriya ta sako wasu tsoffin gwamnoni da aka samu da laifin rashawa.

An sako tsoffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, wato Sanata Joshua Dariye, da Jolly Nyame daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja a Najeriya.

Wannan na zuwa ne watanni uku bayan afuwar da majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasar Muhammadu Buhari ta yi a ranar 14 ga Afrilu, 2022.

Wata majiya daga gidan gyaran hali ta shaida wa jaridar Dailytrust cewa an saki tsoffin gwamnonin ne da misalin karfe 2:15 na ranar Litinin.

Haka kuma an sake wasu fursunoni uku daga gidan gyaran hali da ke Suleja a jihar Nejan Najeriyar.

Nyame dai zai yi zaman gidan yari na shekaru 12 ne bisa samunsa da laifin karkatar da Naira biliyan 1 da miliyan 64 a lokacin da yake gwamnan Taraba, yayin da Dariye ke zaman gidan yari na matsayin shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan daya da miliyan 126.

Matakin da majalisar ta dauka na sakin ‘yan siyasar biyu ya haifar da cece-kuce daga ‘yan Najeriya da kungiyoyin rajin kawo karshen rashawa.

Sojoji Sun Afkawa ‘Yan Shi’a Masu Komawa Gida Bayan Gama Muzahara..

Sojoji da ‘yan sanda sun afka ma Yan Shi’a masu komawa gida bayan sun tashi Daga muzaharar Ashura A Zariya.

Daga Ammar M. Rajab

Kamar yadda aka saba a duk shekara, ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na gudanar da muzaharar Ashura domin juyayi tare da tunatar da al’umma irin kisan gillar da aka yi wa Imam Husaini (AS) da iyalan gidansa da Sahabbansa a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijirar fiyayyen halitta, Annabi (SAWW).

Muzaharar ta bana a Zariya an fara ta ne da misalin kusan karfe 9 na safe, inda aka kammala ta da misalin karfe 10 da mintoci na safe. Muzaharar wacce aka shafe fiye da awa guda ana gudanar da ita, an fara lafiya, aka kuma kammala lafiya.

An fara muzaharar ne daga Kofar Doka, inda aka dumfaro Lemu, daga nan aka mika aka nufi Rimin Kwakwa da Rimin Tsiwa har aka iso Babban Dodo.

Masu muzaharar sun kasance cikin tsari, sanye da bakaken kaya dauke da tutoci da fastoci na alamin dake nuna juyayin ranar Ashura. Suna tafe suna rera baitocin alhini da juyayin kashe Imam Husaini (AS).

Mahalarta muzaharar wanda ya hada maza da mata, yara da manya, matasa da Dattijai da Tsoffi sun kasance cikin natsuwa a yayin muzaharar. Inda al’ummar gari da dama suka yi dafifi suna kallon masu muzaharar a duk inda aka wuce.

A yayin zantawarmu da wasu daga cikin a mahalartar muzaharar, sun jaddada mana manufarsu ta fitowa muzaharar a yau Litinin 10 ga watan Al-Muharram, inda suka ce; sun fito ne domin juyayi da kuma alhini tare da tunatar da al’umma irin abin da ya faru da iyalan gidan Manzon Allah (SAWW) a irin wannan rana. “mun fito ne saboda mu nuna bakin ciki akan kisan gillar da aka yi wa Imam Husain (AS). Sakonmu ga al’umma a wannan rana shi ne mu nuna musu irin kisan gillar da aka yi wa Imam Husain sakamakon ba’adin mutane da suke cewa wannan rana ta farin ciki ce. Mu wannan ranar ta bakin ciki ce saboda abin da ya samu Imam Husain”,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button