IDAN HASKEN RANA TA FITO BA MAI IYA RUFEWA
Muna kaunar Gwamna Zulum saboda Allah, da kuma kokarin sadaukar da rayuwarsa da yayi wajen yakar ta’addancin Boko Haram da mayar da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu tare da tallafa musu, sannan yayi kokari wajen yakar NGOs da suke taimakon ta’addanci da kuma wasu manyan maciya amanar tsaron Nigeria
To amma idan muka dawo ta bangaren aiki wa jama’a da karancin albashin ma’aikata da talauci da yunwa da tsadar rayuwa hakika Gwamna Zulum yana da nasa gazawar, mutanen Borno na kuka dashi, suna fada mana irin wahalan da suke sha, don haka ne ma wasu suke ganin shi Gwamnan Social media ne kawai, to amma watakila wahalar da mutanen Borno suke sha yana da nasaba da illolin yaki na ta’addancin Boko Haram da ya haifar
Mutanen Borno sun fi kowa sanin waye Kashim Shettima wanda aka tsayar takaran Mataimakin Tinubu, sun san bai amfana musu da komai ba a Borno, ga manyan zargin cin hanci da rashawa a kansa wanda wannan Gwamnan ya rufa masa asiri, bai bar komai a Borno ba sai ta’addancin Boko Haram, don haka hatta a jiharsa ba son shi suke ba sai tsiraru
To yanzu suna so suyi amfani da farin jinin Gwamna Zulum domin cimma manufarsu, suna fargaban zasu iya fuskantar matsala daga jama’ar Borno a zaben 2023, shiyasa suke ta yakar duk wani dan siyasa a Borno da ya nuna yana da ra’ayin Maigirma Atiku Abubakar, sunayi a boye har sun zo suna bayyanawa, idan mukami gareka zasu cireka, hatta mayakan Civilian JTF da suka suna goyon bayansu ga Atiku dakatar dasu ake, domin Atiku ne Uban ‘yan Civilian JTF, shi ya fara basu albashi da kudinsa domin a yaki Boko Haram
Wannan ne dalilin da yasa suka fitar da kudi domin su dakile tasirin kamfen din Atiku a Maiduguri, duk wani Kekenapep Naira dubu goma suka biya don kar su fita suyi jigilar magoya bayan Atiku, sukayi ta siyan mutane da kudi domin su hana kamfen din Atiku tasiri, sannan aka dauki hayar ‘yan iskan gari suka raunata magoya bayan Atiku kusan mutum 200 tare da lalata musu ababen hawa
To amma basu sani ba, daga karshe wannan abinda sukayi ya zama alheri ga Atiku, kuma ya kara musu bakin jini da koma baya
Allah Ka tabbatar wa Atiku nasara Amin