.
📻 Labaran Hausa

Koto Ta Yankewa mubarak uniquepikin Hukuncin Bulala 20 A Gadon Bayan Sau

Koto Ta Yankewa mubarak uniquepikin Hukuncin Bulala 20 A Gadon Bayan Sa

Koto Ta Yankewa mubarak uniquepikin Hukuncin Bulala 20 A Gadon Bayan Sa

 

 

 

Koto Ta Yankewa mubarak uniquepikin Hukuncin Bulala 20 A Gadon Bayan Sa

 

 

 

Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin-ashirin kan ɓatanci ga gwamna Ganduje

 

 

Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala ashirirn-ashirin tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu ashirin kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.

 

 

BBC ta rawaito cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kokarin tada fitina a cikin al’umma, sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin na tiktok din su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kan bata masa suna.

 

 

 

Matasan Mubarak Isa Muhammad da aka fi sani da Mu, da Nazifi Muhammad Bala, na shirya gajeren bidiyon barkwanci, inda akasari suke kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane.

 

 

 

Mabarak Unique Pidkin da abokinsa za kuma su share harabar kotun Norman Silance baki dayanta har na tsawon wata guda.

 

 

Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, na gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina,

 

Inda kuma suka amsa laifinsu al’amarin da yasa aka yanke musu hukuncin, Lauya mai gabatar da kara ya ce an kama matasan tun makon jiya inda aka gurfanar da su a gaban kotun, kafin daga bisani kuma aka aika su gidan yari.

 

Matasan dai suna hannun jami’an tsaro har sai sun cika wadannan ka’ido kafin a sake.

 

Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci shi ne lauyan matasan ya kuma gode wa kotun majistaren bisa sassaucin da ta yi musu game da hukuncin, don haka ma basu kalubalanci hukuncin ba.

C.E.O_Founder_OF_Educatetimes _Auwal_Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button