🏥 Magunguna

Nau’ikan Nono Da Ya Kamata Kun Sani Mace Ko Namiji

Nau’ikan Nono Da Ya Kamata Kun Sani Mace Ko Namiji

Nau’ikan Nono Da Ya Kamata Kun Sani Mace Ko Namiji

Kowace mace tana da irin siffar nonon da Allah ya halicce ta da shi.

Wannan yana nufin halittar nonuwan mata ta bambanta.

Wadanda aka fi sani sune kamar haka:

irin wannan nonon halitta ne wanda maza suka fi so, domin yana da ban sha’awa, kuma a tsattsaye yake.

2. Nono daya yafi daya girma (Asymmetrical breasts):

wannan ba wata matsala bace a likitance, dormin dama halittar jikin dan-adam ta dama takan fi ta hagu girma, ko da kuwa ba’a ganin haka a Zahiri. Abubuwan da sake sanya nono daya yafi girma sosai sun hada da ciwon nono (infection), rashin daidaiton sinadarai (hormonal imbalance). rashin lafiyar halittun da suke cikin nono (developmental disorders of breast tissues), rauni a nono (breast injury), matsalolin shayarwa (breast feeding complications) da sauransu.

Dukansu wadannan ana iya magance su ta hanyar shan magani, amma banda rashin lafiyar halittun nono, domin shi sai ta hanyar tiyata ake magance shi.

3. Nono mai siffar zunguru (tubular breast):

wannan shine nono wanda yake da tsawo kamar zunguru ko shantu maimakon dunkulewa wuri daya, kuma akwai tazara tsakaninsu, sa’annan sashen bakin su (areola) suna da fadi sosai. Mafiyan lokaci daya yakan fi daya girma. Irin wannan nonon halitta ne ba cuta take haifar da shi ba, kuma sai ta hanyar tiyata ake magance shi

4. Karamin nono (Athlethic breast):

shine nono maras girma, wanda da kadan ya dara na namiji girma. Wannan shima halitta ne, amma ana iya kara masa girma ta hanyar wasa da shi lokacin saduwar aure (stimulation), atisaye (physical exercise), da kuma cin abinci mai gina jiki (balanced diet).

5. Nono fiye da biyu a kirji (supernumerary breasts):

wasu matan suna da nono uku a kirjinsu. Wannan matsala ce ta halitta (genetic disorder), kuma tiyata ake yi domin magance ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button