FOREX TRADE: Sanina kasuwanchin FOREX dakuma yadda akeyinsa
FOREX TRADE: Sanina kasuwanchin FOREX dakuma yadda akeyinsa

FOREX TRADE: Sanina kasuwanchin FOREX dakuma yadda akeyinsa
Jama’a Assalamu Alaikum Warahamatullahi Barkanku da sake kasancewa daku awannan Shafin Namu Mai Albarka Na
Kasuwar FOREX tasha ban-bam da kasuwar Cryptocurrency ko irn ponzy SCAM irin wanda suke yawo da gari kokuma platform, ma’abota kasuwa suna samun makudan kudade inda wasu dadama suke cewa tafi kasuwar Cryptocurrency kawo kudi.
Ayau a wannan feji namu me suna zamu kawo muku ilimin dake cikin FOREX trading dakuma ban-banchinsa da kasuwar Cryptocurrency sannan da yadda ake Samun kudi ta hanyar FOREX trading.
MENENE FOREX TRADING
Kalmar FOREX kalmace ta turanchi wanda ake nufi da foring exchange da hausa kuma ana nufin sana’ar sanja kudade.
Duk wanda yake a garin kano kokuma ya taba zuwa yasan kasuwar wafa kasuwace wacca ake canjin kudi musali inzaka fita daga kasar da kake zuwa wata kasar dole kana bukatar kudin kasar dazakaje domin biyan wasu buqatun, asukake wannan shi ake kira da FOREX trading.
Sedai shi online FOREX trading anayin sane electronically ma’ana batare daka bude shago ba kawai abun da ake buqata shine wayar android kokuma computer wacca zakana aikin da ita.
Wannan kasuwanchin yanada matukar sauki wajan wahalhalu domin zakayi shine batare da ka bude shago kokuma office ba kana gida kan gadonka zakayi komai sede yasha ban-ban da waccan kasuwanchin daza’ayi physical wato a shago ko office.
Domin shi FOREX trading kana bukatar dabaru dakuma kwarewa kafin kafara shi sannan masu zurfi saboda kasuwanchine wanda ake da kudi kuma inhar baka iya ba kokuma baka da kwarewa kan harkan zaka iya asara me matukar yawa.
