.
📻 Labaran Hausa

Bidiyon da yasa aka kama MubarakUniquePikin kan zagi dacin mutuncin Gwamnan Kano Ganduje Kannywood

Bidiyon da yasa aka kama MubarakUniquePikin kan zagi dacin mutuncin Gwamnan Kano Ganduje Kannywood

Bidiyon da yasa aka kama MubarakUniquePikin kan zagi dacin mutuncin Gwamnan Kano Ganduje Kannywood

👉Abunda kazo Dubawa Yana ƙasa da wanann Bayanin namu Kaja ƙasa da wanann Rubutun Namu Dan Ganinn Abunda kazu Dubawa 👇👇

 

 

FALALAR YIN AURE.

Akwai falala da garaɓasa mai yawa a cikin yin aure bayn mun ji hikmar yin sa daga ciki akwai :
1 Aure sunna ce ta Annabawa Suratu Raadi aya ta 38
2. Allah ya yi umarni da a auran da marasa aure, Maza ko mata ƴanmata ko Zawarawa, Alkur’ani suratu Nuri aya ta 32.

 

 

 

3. Allah ya bada dama ga masu bukatar yin aure ko ƙarin aure, suratu nisa’i aya ta 3.
4. Yana daga cikin ayoyin Allah Daya halicci Maza da mata kuma ya sanya nutsuwa da ƙauna da tausayi a tsakanin ma’aurata, suratu Rum aya ta 21.
5. Hadith yazo daga Maaƙali Bn yasar, Manzon Allah saw yace : ku auri mai soyayya mai haihuwa domin zan yawaici Al’umma da ku. Abu Dauda 2050.

 

 

 

6. Anas ya ruwaito hadith gamai da wasu mutane su uku daga cikin sahabbai waɗanda suka je gidan Annabi saw suka tambayi matan Manzon Allah saw gamai da yadda Manzon Allah saw yake gabatar da ibada, bayan matanAnnabi saw sunyi musu bayani sai suka ga kamar yanayin ya yi musu kaɗan, amma sai suka bada uzri cewa mataƙila shi Annabi saw saboda anyi masa gafara a duk abinda ya gabata da duk wanda ya biyo baya,

 

 

 

amma su akwai buƙatar su ƙara ƙaimi wajan ninka ibada fiye da Yadda Annabi saw yake yi, don haka ɗaya daga cikin su yace shi ba zai yi aure ba, har abada, na biyu yace shi kuma zai dinka sallar dare har abada ba zai ƙara bacci da daddare ba, na uku yace zai dinga azumi kullum ba zai ƙara shan ruwa ba sai da daddare. Sai Annabi saw ya sami labari sai ya kira su yace masu ya ji abinda da ake ce sun faɗa hakane sun faɗa ɗin sai suka ce haka ne amma duk alkhairi muke nufi, sai yake to ku saurara kuji na rantse muku da Allah ni nafi ku tsoran Allah, da kiyaye dokokin sa tare da haka ina azumi ina fashi, ina salla ina bacci, kuma ina aure, don haka duk wanda ya kyamaci sunna ta baya da ni. Bukhari 5063, Muslim 1401.
7. Daga Abdullahi ɗan Maa’ud RA, yace Manzon Allah saw yace mana, :Ya ku taron matasa duk wanda ya sami iko da dama daga cikin ku to yayi aure, domin shi yafi(taimakawa) wajan runtse ido da kiyaye farji. Wanda kuwa be sami iko ba ya dinka azumi, domin zai zame masa kamar ya yi fiɗiya wato kariya daga rinjayan ƙarfin sha’awa. Bukhari 5065.Muslim 1400.

 

 

 

 

Abu zarrin RA ya ruwaito hadith, Annabi saw yace :Idan kuka sadu jima’i da iyalanku za a baku lada, sai sahabbai suka ce, yaya ɗayanmu zai biya sha’awar sa kuma a bashi lada? Sai yace ku bani labari, idan yayi zina ba za a rubuta masa alhakki ba? Sai suka kwarai, sai yace to haka za a bashi lada idan ya kwanta da iyalansa. Muslim 1006. Abu Dauda 1286.

9. Daga Abdullahi ɗan Amr RA yace : Manzon Allah saw yace : Duniya wani jin dadi ce, amma mafi alherin jin daɗinta shine samun mace ta gari. Muslim 1467.
10. Abdullahi ɗan Masud yana cewa Da zai zama saura kwana ɗaya duniya ta tashi, zan so ace nayi aure a wannan lokacin (Musannnaf Ibn abi Shaibah 3/454 )

 

 

 

10. An ruwaito Daga cikin manyan ɗaliban Abdullahi ɗan Abbas wato Abdullahi bn Jubairi yace Abdullahi ɗanAbbas ya tambaye shi shin kayi aure? Sai yace bai yi ba, sai yace masa kayi aure domin mafi alherin wannan al’umma yana da aure. (Wato yana nufin Annabi saw da manyan sahabbansa duk suna da aure don haka idan so kake kabi sunnar su to kayi aure. )

 

 

 

Waɗanan hadisai suna nuna mana yadda sahabbai da tabi’ai suka ɗauki rayuwar aure da muhimmanci,
Musulunci ya haka gudun aure ba tare da wani uzri ba, wasu har tunani suke ko za su yanke gaban su, ko su dandaƙe kansu, akwai cikin sahabbai waɗanda suka yi yinƙurin yin haka Annabi saw ya hana su.( Bukhari 5074. Muslim 1402.) don kada tunanin yin aure ya zo masu, wannan ya saɓawa shari’a da lafiyayyan hankali da kyakkyawar al’ada, ko kuma ya ɗauko

 

 

 

 

wata aƙida ta ƙin aure mace ko namiji ko kuma saboda ya taɓayin aure bai ji da ɗadi ba, ko mace ta yi aure tasha wahala sai kaji suna cewa ni duk maza ko duk mata ba su da kirki don haka ba zan kuma yin aure ba, wannan ba haka bane, ba duk aka taru aka zama ɗaya ba, a sake yin addu’a a gwada za a dace da iznin Allah.

 

C.E.O_Founder_OF_Educatetimes _Auwal_Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button